24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

‘Yan bundiga sun harbe wani Dankasuwa har lahira ana wata 1 kacal kafin auren sa

Labarai'Yan bundiga sun harbe wani Dankasuwa har lahira ana wata 1 kacal kafin auren sa

Wani dankasuwa ya mutu, a sakamakon harbin sa da akayi, yan awoyi kadan bayan an ganshi yana fati da abokan sa. 


Mutumin mai suna KC an ganshi a ranar ashirin da bakwai 27 ga watan Maris,  suna siyayya shi da budurwar da zai aura, kafin a kashe shi. 

dankasuwa
‘Yan bundiga sun harbe wani Dankasuwa har lahira ana wata 1 kacal kafin auren sa

Har ilayau, a ranar dai an ganshi da budurwar da zai aura din, da kuma abokan sa, a wajen bikin  su na gargajiya a gidan Aguluzigbo dake Anaocha, a jihar Anambra. 

Daga baya, a dai wannan ranar 27 ga watan Maris, aka kashe shi da yamma a gaban budurwar tasa wadda zai aura. 
A yadda rahoto ya bayyana, wasu masu bindiga ne suka zo suna so su kwace motar sa, inda shi kuma ya hana su. Nan take suka harbe shi kuma suka gudu da motar. 


A watan Afirilu mai zuwa ne, za’a yi aurensu da budurwar tasa, kafin bikin murnar Easter . 

Sharhin mutane a kan kisan dankasuwan


Gozzy Amah yace :

KC yan fashi ne wadanda suke neman ya basu motar sa, kirar Venza, ku dena wani cewa wadanda ba’a sani ba da Allah,!! Sun kuma gudu da motar. 


Aji Bussu, yace :

sun kashe shi, cikin rashin imani, naji ma ance an kusa bikin sa, ka kwanta cikin salama.

Yan ta’adda sun yi garkuwa da amarya a wajen bikin aurenta, sun kashe wasu 10

A ranar Asabar din da ta gabata ne ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da amarya a wani daurin aure a kauyen Gbacitagi da ke ƙaramar hukumar Lavun a jihar Neja, inda suka kai farmaki a wasu ƙauyukan yankin tare da kashe wasu mutanen ƙauyen 10, wasu daga cikinsu baƙi ne a wurin daurin auren.

Dukkanin kayayyakin da aka kawo domin bikin auren da kuma kuɗi ‘yan ta’addan sun kwashe. ‘Yan bindigar da yawansu ya kai 100, da ke kan babura dauke da nagartattun makamai da suka hada da bindigogi ƙirar AK47 sun afka wa al’ummar .

‘Yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da wasu manya-manyan shanu tare da sace kayan abinci a ƙauyukan da suka kai hari.

Wasu ƙauyukan da aka mamaye a cewar rahoton sun hada da Egbako, Ndaruka, Ebbo, Ndagbegi, Tshogi, Gogata da Ndakogitu Tsonfadagabi, Kanko da Gbacitagi.
An gano cewa ‘yan ta’addan sun maƙale a Akere, inda aka ce gadar da ta hada al’umma da Wushishi ta ruguje.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

https://youtube.com/watch?v=Awk-bNuRKhs%3Ffeature%3Doembed

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe