35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Jerin Sunaye:Amurka ta fallasa jerin sunayen ‘yan Najeriya 6 dake daukar nauyin Boko Haram

LabaraiJerin Sunaye:Amurka ta fallasa jerin sunayen 'yan Najeriya 6 dake daukar nauyin Boko Haram
d130ab49386bbdd8
Amurka ta fallasa jerin sunayen ‘yan Najeriya 6 dake daukar nauyin Boko haram

A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya fitar, ‘yan Najeriyar da aka sanyawa takunkumin sun yi “wajen taimakawa, da daukar nauyi, ko bayar da tallafin kudi, kayan aiki, fasahar kere-kere, kayayyaki ko ayyuka ga kungiyar Boko Haram.

Ga Jerin sunayen:

  • Abdurrahman Ado Musa
  • Salihu Yusuf Adamu
  • Bashir Ali Yusuf
  • Muhammed Ibrahim Isa
  • Ibrahim Ali Alhassan Surajo
  • Abubakar Muhammad

‘Yan Najeriyar da aka sanya wa takunkumi an yanke musu hukunci ne tun a Dubai

A cikin sanarwar an bayyana matakin da Amurka ta dauka ya biyo bayan tuhumar da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi na yanke hukunci, da kuma bayyana sunayen ‘yan Najeriya da aka lissafa wadanda ake tuhumar su da laifin tallafawa ta’addanci.
Labarun Hausa ta kuma ruwaito cewa, tun da farko wata kotun daukaka kara dake birnin Abu Dhabi da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yanke wannan hukuncin. Inda Ake tuhumar su da laifin tallafawa kungiyar Boko Haram ta hanyar ba da damar aika kudade daga Dubai zuwa Najeriya domin kara ta’azzara ta’addanci.

Biyu daga cikin su an yanke musu hukuncin rai da rai

Biyu daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, Surajo Abubakar Muhammad da Saleh Yusuf Adamu, an yanke musu hukuncin daurin rai da rai. Sauran hudun da suka hada da: Ibrahim Ali Alhassan, AbdurRahman Ado Musa, Bashir Ali Yusuf da Muhammad Ibrahim Isa an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekaru goma.


Neja: ‘Yan sanda sun cafke wani mai safarar kayan abinci ga ‘yan bindiga

Hukumar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wani Umar Dauda mai shekaru 20 wanda ya ke kai wa ‘yan bindiga abinci a jihar. Jarudar Punch ta rahoto

Ya shiga hannu bayan samun bayanan sirri
A wata sanarwa wacce kakakin hukumar, Wasiu Abiodun, ya sanya wa hannu, an cafke wanda ake zargin ne bayan samun bayanai daga mazauna garin.

An yi kamen ne a ranar 16/03/2022, da misalin ƙarfe 11 na dare bayan samun
bayan samun bayanan sirri cewa ana yawan ganin wanda ake zargin da kai abinci da ababan sha ga ‘yan bindiga a ƙauyen Kapako cikin ƙaramar hukumar Lapai. A cewar sa

Abiodun ya bayyana cewa an tura jami’an ‘yan sanda da ke Lapai tare da haɗin guiwar ‘yan sakai zuwa ƙauyen, inda bayan dogon nazari da sa ido, su ka cafke wanda ake zargin.
Kakakin na ƴan sandan ya ƙara da cewa an samu kayyayakin abinci da kuɗade a hannun sa yayin binciken..

Ya bayyana cewa:

An samu waɗannan abubuwan a hannun sa; sunƙin burodi guda 6, kwalbar fearless guda 4, gwangwanin maltina 4, ɗauri huɗu na busashshen ganye da ake zargin wiwi ce, shinkafa da wake da kuma kuɗi.
Abiodun ya kuma ƙara da cewa a yayin da a ke gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa yana kai wa ‘yan bindigan kayan abinci sannan su na zuwa har gidan sa a ƙauyen domin amsar kayan abincin.

Ya ƙara da cewa wannan shine karo na huɗu da wanda ake zargin ya ke safarar abinci ga ‘yan bindigan kafin ya shigo hannu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe