22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Wani Saurayi ya wallafa hotunan kyakyawar matarsa, wacce suka fara soyayya tun tana karama

LabaraiWani Saurayi ya wallafa hotunan kyakyawar matarsa, wacce suka fara soyayya tun tana karama
frh3
saurayi ya wallafa hotunan kyakyawar matarsa wacce suka fara soyayya tin tana karama

Saurayi da budurwa sun shafe tsawon shekaru suna soyayya

Labarin soyayya mai kayatarwa na wani saurayi da matarsa ya sa mutane tofa albarkacin bakin su a shafukan sada zumunta.
Saurayin ya wallafa wasu daga cikin hotunan su a shafin sada zumuntar zamani na TikTok inda yake nuna yadda ya hadu da matarsa lokacin tana ƙarama har zuwa lokacin girman ta inda ta zama kyakkyawar mace, wacce ta zama matarsa a yanzu.

Ya wallafa hotunan su tun daga farkon soyayyar har zuwa aure

eety5

Saurayin Ya wallafa kyawawan hotunan su na ‘yanzu da da’ tare da kwatanta ta a matsayin babbar abokiyar sa.

Da yake mayar da martani ga bidiyon, wani mai amfani da shafin Instagram:

@nikkydaves ya ce: “wannan cin zarafin yara ne ai !! Cin zarafin yara!! tun ba ta kai shekara ba ya fara rainon ta daga baya kuma ya yi wuff da ita”.

@thesaviour_ofparty, “Kamar yadda wannan gayen ya raini yarinyar nan tun tana karama, ya jira har ta girma ya aure ta??? Ah! ’Yan Arewa sune BABBAR MATSALAR NIGERIA.”

@the_3k_shop, “ya so ta tun tana karama ya jira ta ta girma sannan ya aureta ban sani ba ko wannan abu ne mai kyau ko mara kyau amma dagani wannan abu ya yi musu dadi kuma naji dadi. game da hakan.”

@iamnnedimma, “Regina ma saidai ta sara musu”.

@chiskyetc, “A kasashe masu hankali zai kasance cikin jerin masu laifi amma sauran addinai a cikin ƙasashe za su ga hakan kamar ba laifi ba ne “chukwuabiama”

Ina shirin siyar da motata don daukar nauyin karatun saurayina, ya cancanci hakan, Budurwa

Wata budurwa ta bayyana yadda za ta biya wa saurayin ta kuɗin digiri na biyu wato ‘masters’. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Budurwar za ta fara yi masa kasuwanci


Budurwar ta ƙara da cewa za ta yi amfani da ragowar kuɗin wajen fara wa saurayin na ta kasuwanci wanda a cewar ta ya cancanci komai.

Ina son na siyar da motata domin biyawa saurayi na kuɗin zangon ƙarshe domin ya samu ya kammala digirin sa na biyu.
A yayin wata zantawa da TUKO.co.ke, Turamuhawe, ta bayyana cewa ita ta aminta da cuɗeni in cuɗeka.

Na ga mazaje da yawa waɗanda su ka yiwa ‘yan matan su abubuwa da dama saboda suna ƙaunar su, sannan ni na yarda da cuɗeni in cuɗeka. inji Turamuhawe.
Ina son na siyar da motata domin biyawa saurayi na kuɗin zangon ƙarshe domin ya samu ya kammala digirin sa na biyu. Ina tunanin zan yi amfani dansairan kuɗin wajen fara masa ƙaramin kasuwanci yayin da ya ke neman aiki tunda yana son yayi abinda ya karanta. Matashin sarki ya cancanci komai.

Mutane sun tofa albarkacin bakin su


Bayan ta yi wannan wallafar a shafin Twitter, ga abinda mutane ke cewa:

Joansheenah ya ce: “Cikin hawaye abin zai ƙare.”
Brökë_C3lëbrïty ya ce: “Idan har da gaske ne to ina so na zama saurayin ki. Ina mamaki yadda wani ya ke ƙoƙarin neman digiri na biyu amma bai da aikin yi.”

Marvin k ya ce: “Gaskiya ka da ki siyar da motar ki. Idan zai yiwu ki amshi bashi, sannan ki yi amfani da motar ki a matsayin jingina, kowane banki zai baki bashin kuɗi daganan sai ki dinga biya a hankali a hankali, saboda za ki buƙaci motarki sannan saurayin ki yayi sa’ar samun ki.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe