24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Ramadan 2022: Jirgin ƙasan Harami mai matuƙar gudu zai yi safarar sama da fasinjoji 625,000 yayin azumi

LabaraiRamadan 2022: Jirgin ƙasan Harami mai matuƙar gudu zai yi safarar sama da fasinjoji 625,000 yayin azumi

Kamar yadda mujallar Saudi gazette ta ruwaito, jirgin kasa na masallatan Makka da Madina mai tsakanin gudu, zaiyi aiki sau hamsin 50 a rana, lokacin azumin Ramadan.

An kaddamar da wannan doka ne domin yin jigilar mutane dubu dari shida da ashirin da biyar 625,000, daga alhazai na gida da wadanda suka zo daga waje, domin gudanar da Umarah a watan na azumi, mai tsarki. 


Haramain Hight-speed Railway, wani wata hidima ce ta jigilar mutane a jirgin kasa, wadda ta hada manyan buranen Makka da Madina, masu tsarki, wadda take da tashoshi a, Kinga Abdallah Economic City, KAEC, Jidda Airport wadda take a tsakiyar birnin Jidda. 

jirgi
Ramadan 2022: Jirgin ƙasan Harami mai matuƙar gudu zai yi safarar sama da fasinjoji 625,000 yayin azumi

A fadar wata majiya daga hukumar, tace, jigilar zata karade hanyoyin Makka da Madina ne, zuwa da dawowa, inda zata ratsa ta, babbar cibiyar ta dake  SulaymaniyahJidda, da kuma tashar KAEC dake Rabigh. 


Haka kuma, mahukuntan zasu samar da jigilar daga filin jirgin sama na  kasa-da- kasa na King Abdulaziz, dake Jidda, zuwa buranen Makka da Madina, wanda har ilaihi yau dai zai ratso ta KAEC din dai. 


Hukumar dai, ta sake bayyawa cewa, yan watanni da suka wuce, an sami karin bukatuwar aikin jirgin da kaso 35. 
Hukumar tayi kiyasin cewa, ayyukan jirgin zasu lunku, idan har ya ci gaba da samun tagomashi a lokacin azumin Ramadan. 


Da akwai yiwuwar kuma wannan hasashen ya kasance daidai, idan akayi la’akari da dandazon mahajjatan da zasu ziyarci kasar daga fadin duniya, domin gudanar da Umarah a wata Ramadan din. 


A shekarar 2021 ne dai jirgin mai tsabar gudu ya dawo aiki, bayan tsaikon da ya samu na tsawon shekara daya dalilin cutar annobar COVID-19. 


A waccan shekara, shugaban hukumar kula da sufuri, Rumaih bin Mohammed Al-Rumaih, ya bayyana cewa, jirgin kasa na masallatan Makka da Madina, ya shirya tsaf domin jigilar alhazai a lokacin aikin hajji da Umarah.

Amma za’a ci gaba da bin dokokin kariya na annobar corona.

Hukumomin Saudiyya sun ƙwace jabun ruwan zam-zam kimanin katan ɗari huɗu a Makkah

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kafafen yada labarai na kasar Saudiyya suka rawaito cewa hukumomi a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya sun ƙwace fakitin Zam-zam sama da 400 wadanda ake zargin na jabu ne kuma ba za a iya sha ba.

A cewar jami’an birnin, an adana kwalaben a cikin yanayin da bai dace da ka’idoji ba kuma sun keta ka’idojin tsabta. An kuma bayyana cewa an cika kwalaben da ruwan da ba a san asalinsa ba kuma an yi wa ruwan lakabi da ruwan zamzam.

Amma an yi sa’a, hukumomin birnin a Saudiyya sun yi nasarar gano su tare da lalata su kafin su yaɗa su tare da sayar da su a kasuwannin gida. Za a ɗauki tsauraran matakan shari’a a kan wadanda suka keta dokar don hana faruwar irin wannan lamari.

A baya-bayan nan ne hukumomin Saudiyya a birnin Makkah suka ƙara yawan ayyukan sa ido a shirye-shiryen azumin watan Ramadan da ake sa ran za a fara a ranar 2 ga watan Afrilun wannan shekara.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe