27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ramadan 2022: Sunayen limamai 6 da zasu jagoranci sallar Taraweehi da Tahajjud a Masjidul Haram

LabaraiRamadan 2022: Sunayen limamai 6 da zasu jagoranci sallar Taraweehi da Tahajjud a Masjidul Haram


Hukumomin kasar Saudiyya sun fitar da jerin sunayen limaman da zasu jagoranci sallar Tarawi da Tahajjud a masallacin Makka na azumin wannan shekarar. Wannan jerin sunayen an fitar da su ne a shafin tweeter na Haramain Sharifain, a ranar 23 ga watan Maris. 

Sunayen Limaman da zasu jagoranci sallar Tarawi da Tahajjud a masallacin Makka 

Sunayen Limamai shida 6 wadanda zasu jagoranci sallar a masallacin haramin Makka, lokacin azumin 2022, wadda za’a fara a watan Afirilu, sune kamar haka : 

1. Sheikh Abdullah Awad Al Juhany

2.Sheikh Abdur Rahman Al Sudais

3.Sheikh Saud Al Shuraim

4.Sheikh Maher Al Muaiqly

5.Sheikh Sheikh Yasir Al Dawsary

6.Sheikh Bandar Baleelah


A yadda jerin sunayen suka zo, ya nuna cewa babu wani Limami daga wajen kasar da zai shiga jerin limaman a wannan shekarar . 


Haka kuma, jawabin yadda kowanne limami zai yi sallah da lokacin da zaiyi ta, shima hukumar ta fitar da jadawalin sunayen limaman dakidaki. 


Yadda jadawalin tsarin sallar Tarawi na masallacin Harami yake

jadawalin tahajjud da taraweehi
Jadawalin limancin sallolin Tarawi da Tahajjud ,da sunayen limaman

A baya, Musulmai na duniya sunyi murna kwarai, kasantuwar samun albishir na cewa, za’a gudanar da sallar Tarawi da Tahajjud a masallatan Makka da Madina, ba tare da fashin ko daya ba. Shugabancin hukumar kula da masallatan Makka da Madina ne ya sanar cewa, gabaki daya da yan kasa da baki duk zasu halarci sallolin a duka masallatan guda biyu. 


Wannan kyakkyawan albishir ne ga daukacin musulman duniya, idan aka yi la’akari da yadda a baya a shekarar 2021, aka hana kowa yin sallolin, in banda wasu yan kalilan, wanda ya hada da mahukuntan hukumar kula da masallatan, da kuma wasu yan kadan daga al’ummar gari, saboda a wancan lokacin an sanya dokar zaman gida, kuma an hana baki shiga kasar domin dakile yaduwar cutar COVID-19. 


Mahalarta sallar dai ana da bukatar su kiyaye ka’idodin na kariya, zasu bada tazara, sannan kuma zasu nuna takunkumin hanci a kofar bincike kafin su shiga masallatan.

An amince da yin buda baki a masallacin Harami da na Annabi(SAW) bayan shekaru 2 da dakatarwa

A yayin shirye-shiryen maraba da watan Ramadan, shugaban hukumar kula da masallatan harami guda biyu ya sanar da cewa an bayar da izinin gudanar da liyafar buɗa baki a masallacin Harami bayan dakatarwar da aka yi na tsawon shekaru biyu sakamakon annobar COVID-19, theislamicinformation.com ta ruwaito.

An kuma sabunta izini ga masu samar da abinci mai saurin gaske a wuri mai tsarkin.

Fadar shugaban ƙasar ta kuma sanar da cewa an bayar da izinin dawo da buɗa baki a masallacin Annabi da ke Madina.

Ana sa ran masallatan Harami guda biyu za su tarbi ɗimbin masu ibada a lokacin Umrah a Masallacin Harami da ziyartar masallacin Annabi a cikin watan Ramadan, wanda za a fara a farkon watan gobe.

Hukumomin Saudiyya sun sassauta dokokin gudanar da aikin Umrah a baya-bayan nan bayan wani mataki da masarautar ta dauka, wanda kuma ya sassauta takunkumin hana yaɗuwar cutar COVID-19.

Wasu daga cikin matakan kariya da aka soke sun haɗa da soke izinin yin Sallah a Masallacin Harami da kuma soke gwajin riga-kafi ga dukkan mahajjata masu shiga Masallacin Harami guda biyu.

Bugu da kari, ma’aikatar Hajji da Umrah ta kuma soke rajistar bayanan riga-kafin ga al’ummar Musulmi a ƙasashen waje domin samun izinin Umra wanda a baya ya zama dole.

Wajabta nuna gwajin PCR mai kyau don shigar da wuraren ibadar guda biyu shima an ɗauke shi.

Jaridar Okaz ta bayar da rahoton cewa, musulmin da aka yi musu allurar riga-kafin da waɗanda ba a yi musu allurar ba, a yanzu za su iya gudanar da aikin umrah a masallacin Harami bisa wasu sharuɗa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe