24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

In Ajali ya yi kira:Zuweira budurwar da Likitoci suka tabbatar da mutuwarta ta farfado sa’o’i kadan ta sake cewa ga garin ku

LabaraiIn Ajali ya yi kira:Zuweira budurwar da Likitoci suka tabbatar da mutuwarta ta farfado sa'o'i kadan ta sake cewa ga garin ku
9d5831d1a82fec32
Zuweira budurwar da likitoci suka tabbatar da mutuwarta sa’o’i kadan ta sake cewa ga garinku

Likitoci sun sanar wa ahalinta mutuwar ta,jim kadan bayan sun ce ta farfado

Wata budurwa mai suna Zuweira da rahotanni suka bayyana mutuwarta, daga bisani kuma ta farfado ‘yan mintuna kadan kafin a binne ta, ta sake mutuwa. likitocin asibitin Ridge dake Accra kasar Ghana sune suka tabbatar da mutuwar budurwar a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris.
A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana,an ga Antin zuwaira, Rabu wacce ita ce ta bada bayanin cewa Likitoci sun tabbar da mutuwar Zuweira a inda aka shirya yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulmi ya tanada, Rahotanni daga Ghanaweb. Ta ce an shirya duk wani shiri da ya dace kawai likitoci su ka kira cewa Zuweira ta farfado.

Wata ‘yar uwarta ita ta sanar da labarin mutuwar ta a shafin ta na Facebook

Rabi Dan-Alpha Sharubutu ta tabbatar da cewa diyarsu ta sake rasuwa, tana mai cewa:

Na gode wa kowa da kowa bisa addu’ar da kuka yi wa ‘Yar uwata. Amma ta koma ga mahaliccin ta yau, Allah ne mafi sani. Allah ya sa ta huta, ta ce.

Mutane da dama sun mayar da martani tare da kaduwa game da wannan wallafa na Antin Zuweira.

Ga kadan daga cikin martanin mutane:

Gimbiya Umma ta ce: ”Allah ya jikanta Yasa Aljanna ce makoma.”

Adam Ibrahim ya ce:Allah ya jikan ta da Rahama.”

AlhajiGaza Gudliving ya ce: ”Allah Ya jikanta da Rahama”

Abdul Rashid Goodman ya ce. : ”Hmm. Allah ya sa ta huta .”
Jay Bansi Rockafella Gh ya ce:Ya Allah muna mika sakon Ta’aziyya mu ga dukan iyalan ta. Ina rokon Allah ya kara muku hakurin Rashi Allah ya jikanta da rahama. Amin yaa Allah


Gaggawa: Wani mutumi ya bayyana cewar ana saurin binne gawa tun da sauran numfashi kamar yadda aka kusa yiwa Dansa

Wani mutumi a jihar Kano, mai suna Nura Ahmad Mahmud ya ce, gaggawar da mutane ke yi wajen kai gawa kushewa da ga zarar an ga numfashin mutum ya dauke, hakan ne ke sanyawa a rufe wasu da sauran numfashin su.
Mutumin, ya bayyana hakan ne, a wata zantawa da akayi dashi a gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Alhamis.
Inda ya kara da cewa “Ni kaina irin wannan al’amarin ya taba faruwa da dana, an fada mana cewar ya mutu, amma saboda jinkiri da mu ka yi wajen shirya shi don kaishi kushewa, hakan ne ya ceto rayuwar yaron,yanzu haka yaron yana nan yana ci gaba da rayuwa yana yawon sa ko ina”.

Mutumin ya kara da cewa “ shekarar mu ashirin, Allah bai azirtamu da haihuwa ba, kwatsam ta samu ciki,ranar da ta haihu, sai likitoci su ka shaida mana cewar, jaririn fa ba zo da rai ba, ba muyi gaggawar kaishi makabar ta ba , jim kadan sai muka lura kafafunsa na motsi”. A cewar Nura Ahmad
Nura Ahmad Mahmud, ya shawarci al’umma, da su rinka jinkirta binne ‘yanuwan su zuwa wani lokaci, domin gujewa binne gawa da rai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe