Don guje wa barna, iyaye su daina yi wa yaransu aure gab da watan Ramadan, Sheikh Abdallah Gadon Kaya

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Don guje wa barna, iyaye su daina yi wa yaransu aure gab da watan Ramadan, Sheikh Abdallah Gadon Kaya
Don guje wa barna, iyaye su daina yi wa yaransu aure gab da watan Ramadan, Sheikh Abdallah Gadon Kaya

Babban limamin masallacin Juma’a na Usman Bin Affan da ke Gadon Kaya a Jihar Kano, Dr Abdallah Usman Umar, ya ce don gujewa barna barna tsakanin sabbin ma’aurata, ya kamata a tsagaita daga yin aure idan ana saura mako daya azumi.

A cewarsa, ko da kuwa auren ya matso, zai fi dacewa a kai shi can gaba, zuwa bayan watan azumin, Dala FM ta ruwaito.

Don guje wa barna, iyaye su daina yi wa yaransu aure gab da watan Ramadan, Sheikh Abdallah Gadon Kaya
Don guje wa barna, iyaye su daina yi wa yaransu aure gab da watan Ramadan, Sheikh Abdallah Gadon Kaya

Ya yi wannan bayanin ne a wani shiri na Rayuwa Abar Koyi, wanda gidan rediyon Dala FM, Kano, ya shirya wanda suke yi a duk ranar Juma’a da misalin karfe 9 na safe.

Kamar yadda ya shaida:

“Amare da angwaye ya kamara su guji yin aure kafin watan Ramadan don gudun fadawa tarkon shaidan da kuma aikata barna ta hanyar karya azumi.”

Ya ci gaba da cewa:

“Dayawan masu sabbin aure suna zuwa wuri na neman fatawa saboda sun karya a azumi a cikin watan Ramadan.”

Hakan yasa ya ja kunnen iyaye da su kiyaye aurar da yaransu aka gab da watan Ramadan, musamman ana saura mako daya.

Ya kamata masu aure su dinga fita cin Shawarma da Pizza da matansu, Dr Abdallah Gadon Kaya

Dr Abdallah Usman Umar, limamin masallacin Usman Bin Affan da ke Unguwar Gadon Kaya, ya ce ya kamata magidanta su dinga fita tare da matansu zuwa wurin cin abinci don hakan ya na kara dankon soyayya sannan kuma kyautatawa ce ta masoya.

Dakta Abdallah ya kara da cewa idan namiji yana yin hakan zai kara shakuwa tsakaninsa da matarsa.

Ya shaida hakan ne a wani shiri na Dala FM na Rayuwa Abar Koyi da ya gudanar a ranar Juma’a.
Kamar yadda yace:

“Magidanci zai samu shakuwa da kyautatawa tsakaninsa da matarsa idan har yana fita tare da ita zuwa wurin cin abinci tare da zagawa da ita cikin gari musamman wuraren da bata sani ba.”

Ya kara da cewa:

“Bai kamata mazajen aure su dinga yin saurin fushi tsakaninsu da matansu ba, ya kamata su dinga hakuri maimakon yin hakan.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

This Post Has One Comment

  1. mustapha saidu rungumi

    aslm .dangane da abinda malam ya fada to lallai ya kamata iyaye gujewa ya`yan su aure lokacin na saura sati daya ayi azumi .
    ba karamar 6arna ake tafkawa ba ga wandanda sukayi aure awannan yanayi ,da yawa wasu na kare azumin su sanadiyyar yin aure awannan lokaci. masu ilmi ke gane azumin su ya kare kuma sunsan abinda ya janyo musu faruwar haka ,to amma wanda baya da ilmi to ya zaisan azumin sa ya kare tuda ya san matar sa matar sa ce ai komai yayi gani yake dai-dai ne ko acikin watan ramadana . don haka ina goyon dr.Abdullahi usman gadon qaya akan jan hankali ga iyaye da ma su kansu ma`aurata
    Allah yasa mudace Ameen.

Rubuta Sharhi