24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Tsadar kayan abinci: ‘Yan kasuwa su taimaka su rage farashin kayan abinci kafin Ramadan, Sarkin Musulmi

LabaraiTsadar kayan abinci: 'Yan kasuwa su taimaka su rage farashin kayan abinci kafin Ramadan, Sarkin Musulmi

Sarkin musulmi, Muhammad Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya akan kawo mafita dangane da tashin farashin kayan abinci a kasar nan, LIB ta ruwaito.

Yayin jawabin rufe taron gasar karatun Al’Qur’ani mai girma da aka yi a Jihar Bauchi, ranar Asabar, 26 ga wata Maris din shekarar 2022, Sultan ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi gyara akan tabarbarewar tattalin arziki musamman ganin watan Ramadan ya karato.

sarkin musulmi
Tsadar kayan abinci: ‘Yan kasuwa su taimaka su rage farashin kayan abinci kafin Ramadan, Sarkin Musulmi

Basaraken ya tunatar da shugabannin siyasa cewa ‘yan Najeriya sun zabe shi ne don su yi musu aiki, ya roki masu sayar da kayan abinci akan su sassauta farashin kayan abinci lokacin azumi.

Kamar yadda yace:

“Ina tunanin ya rage mana akan mu hade kawunanmu don yin aiki akan tashin farashin kayan abinci, saboda kowa ya samu ya siya a lokacin Ramadan.

“Na yarda da cewa wannan bukatar bata gagari gwamnati ba. Don mun zabe su ne don suyi mana aiki ba wai muyi musu aiki ba.

“Ina son tunatar da ‘yan kasuwa cewa su ji tsoron Allah akan yadda suke sayar da kayan abinci. Kuma sai Allah ya tambayesu a ranar Tashin alkiyama.

“Maimakon kara farashin kayan abinci da sauran abubuwa, suyi kokarin rage farashin don samun rahamar Ubangiji.”

Yayin tsokaci akan zaben 2023 da ke karatowa a 2023: ya kada baki ne ya ce:

“Kada ku dage ku ce ko a mutu ko ayi rai, saboda Ubangiji ya riga ya san ko wanene zai lashe zaben a ko wanne mataki.”

Kisan Musulmi a Jos ka iya haifar da mummunan rikici – Sarkin Musulmi

A jiya ne dai Mai Girma Sarkin Musulmi, Alhaji Mohammed Sa’add Abubakar, ya yi gargadi game da rikicin kabilanci a kasar nan, biyo bayan kisan da aka yiwa al’ummar Musulmi a jihar Filato, inda aka kashe akalla mutane 25 da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga wajen taron zikiri da suka je jihar Bauchi a ranar Asabar.

Idan ba a manta ba wasu mutane daa ake zargin matasan Irigwe ne sun kaiwa motocin matafiyan guda biyar hari, inda suke kan hanyar su ta komawa garin Ikare dake jihar Ondo, bayan halartar zikirin shekara-shekara da ake gabatarwar a jihar Bauchi, wannan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 25 da kuma da dama da suka ji ciwo, yayin da wasu kuma aka neme su aka rasa.

Sarkin Musulmin ya yi maganar a ranar da gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar hana fita a kananan hukumomi uku na jihar da suka hada da Bassa, Jos ta Kudu, da kuma Jos ta Arewa, sakamakon rikicin.

Wannan ya biyo bayan umarnin da Sufeto Janar na hukumar ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya bayar jiya, akan ayi gaggawar kai dakarun ‘yan sanda yankin na jihar Filato don kamo wadanda suka aikata wannan mummunan abu kuma su tabbatar da zaman lafiya.

Wannan dai na zuwa ne bayan kungiyar Kiristoci ta CAN yankin jihar Filato da kuma kungiyarr Fulani ta kasa (Miyetti Allah) suka fito suka yi Allah wadai da wannan lamari, suka kuma bukaci gwamnatin tarayya ta nemo wadanda suka yi wannan aika-aika don su fuskanci hukunci.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe