29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Gaskiyar bayani dangane da batan dan Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami

LabaraiGaskiyar bayani dangane da batan dan Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami

An samu kishin-kishin din wani labari na cewa an sace dan ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, mai suna Al’amin Isa Ali Pantami, a ranar Alhamis a kusa da ginin NITB da ke Jihar Bauchi, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Sai dai abinda ya hana LabarunHausa.com wallafawa shi ne yadda jami’an tsaro, babban limamin masallacin Juma’an Sheikh Isa Ali Pantami da ma wasu almajiransa amma duk sun ce basu da masaniya dangane da labarin.

PANTAMI
Gaskiyar bayani dangane da batan dan Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami

Kwatsam a yammacin Asabar sai ga labari ya bayyana, na cewa an gano dan ministan, kuma har Aminiya ta yi rahoto akan lamarin.

Kamar yadda majiyar tace:

“Daya daga cikin malaman yaron ta shaida wa wakilin Tsakar Gida cewa sun fito daga gidan su, ya dawo yanzu. An same shi a Dambam, wadanda suka sace shi sun ajiye shi a shingen binciken jami’an tsaro, daga nan aka dawo da shi gida.”

Majiyar ta ci gaba da cewa:

“Da dare aka shaida mana cewa an sace shi, amma mun gode wa Allah da yasa suka yar da shi.”

Babban limamin masallacin Juma’ar Sheikh Isa Ali Pantami, Imam Hussaini ya tabbatar da cewa yanzu haka yaron yana gida.

Sai dai, jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi, Muhammad Ahmad Wakil, ya ce ba a kai musu rahoton ba.

Jama’a su na ta zungurin Sheikh Pantami a soshiyal midiya akan rusa kukan da ya yi

Sheikh Isa Ali Pantami, ministan sadarwa ya na shan cece-kuce bayan wani kuka da yayi. An gan shi a wani bidiyo wanda ya ke wa’azi akan yadda mutane su ke dibar kaya daga wani shago da ya yi gobara a Abuja su na tserewa.

Yana tsaka da wa’azin ne shehin malamin ya fashe da kuka dauke da hankici yana share hawayensa.

Kowa ya san yadda ake ta zungurin malamin addini kuma ministan sadarwa, Pantami a kafafen sada zumunta tun bayan masu hare-hare sun ci gaba da kai farmaki garuruwa yayin da ya yi shiru ba tare da ya yi magana ba a wa’azin da ya ke yi ko kuma a shafukansa na kafafen sada zumunta kamar yadda ya saba yi a baya.

Kowa ya san yadda malamin ya saba da caccakar gwamnati a baya yana janyo ayoyi da hadisai wani zubin har kuka ya ke yi kafin ya dare kujerar minista.

Mutane da dama sun dinga wallafa maganganun da Pantami ya yi a baya tare da bidiyoyinsa wadanda yake caccakar gwamnati inda mutane ke korafin meyasa yanzu ba ya magana tunda ya samu matsayi wanda zai iya fadi kuma a ji shi.

Akwai wadanda su ke zargin ya na kare kujerarsa ta minista ne don gudun a fatattake shi.

Daga karshe dai Pantami ya fito ya yi magana inda ya yi bayanin cewa su na zama da manyan mutane masu ruwa da tsaki a harkar tsaro kuma su na ba su shawarwari masu amfani amma ba abu ne da za a fito a bayyana wa jama’a ba.

Wasu mutane sun musanta wannan maganar Pantami yayin da wasu su ka dinga yi masa fatan alkhairi domin kasantuwarsa a irin wannan matsayin watakil ba karamar hidima ya ke yiwa addinin Allah ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe