27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Masana Ilimin Addini da Likitoci sun yi raddi ga matar da ta haifi Dabba a garin Zariya

LabaraiMasana Ilimin Addini da Likitoci sun yi raddi ga matar da ta haifi Dabba a garin Zariya
JAKIN
Masana ilimi da likitoci sun yi raddi ga matar da ta haifi dan Dabba a zariya

Matar da ta haifi Dan Dabba a zariya lamarin yaja hankulan mutane
A ranar litinin din makon da ta gabata ne wata mata mai suna murja ta bayyanawa duniya cewar ta haifi da mai siffar Akuya da,kofaton Doki,wannn lamari ya farune a unguwar Tudun Wada Zaria dake garin kaduna.
Wannan lamarin ya ja hankulan mutane musamman a Arewacin Nijeriya saboda kasancewar sa bako kuma sabon lamari a zamantakewar dan Adan kuma a al’adance ace Dan Adam ya haifi dabba.
Hakan ya sa manema labarai ba su yi kasa a gwiwa ba wajen jin ra’ayin masana akan faruwar wannan lamari.

Sheikh Aliyu Abdullahi Teleks babban malami kuma babban limami a masallacin Juma’a dake Tudun Jukun Zariya kuma shugaban majalisar malamai ta JIBWIS a jihar Kaduna a yayin da ake zantawa da shi ya yi wa manema labarai bayani akan lamarin haihuwar Dabba da Murja tayi a garin Zariya.

Wani malami ya magantu game da faruwar lamarin

“Gaskiya akwai shakku sosai a cikin wannan lamarin idan aka yi dubi da koyarwar addinin Islama za a ga cewar babu yadda zai yiwu a ce wani jinsi ya haifi wani jinsi duk da cewa akwai masuyin sihiri amma duk da hakan wannan lamarin akwai shakku a ciki ”.
Shehin malamin ya ja hankalin jama’a akan irin wannan sihirin inda ya bayar da misali da wani mutum da yace zai fitar da maciji a wata hanya da ake yawan hadari a zariya daga karshe lamarin ya tabbata ba gaskiya ba surkulle ce kawai, wannan ma nan gaba kadan jama’a zasu gane gaskiyar lamarin tunda ance ba haihuwar abin ta yi ba kamar yadda aka san ana haihuwar Da ta al’aura wannan,mai bayar da magani ne suka kira ta shafa cikin kawai sai ga Dabba a matsayin shine abin dake cikin don haka malamin yayi kira da mutane su guji gasgata irin wadannan abubuwan daka iya zama shirka.

Likitoci ma sun tofa nasu albarkacin baki game da lamarin

Haka zalika manema labarai sun nemi jin ta bakin likitocin kimiyar Dan Adan na asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ( ABUTH)

Inda aka sami zantawa da Dakta Hasan Abubakar wanda shine shugaban likitoci reshen asibitin Tudun Wada Zariya wanda ke karkashin asibitin koyarwa na jami’ar ta Ahmadu Bello Zariya.
Likitan ya ce: ” maganar Bil Adam ya haifi wani jinsi ba Mutumba a yadda aka samu fadadar ilimi hakan ya saba wa hankali mun san dai akan sami mutum ya haifi Da babu kafa ko kuma babu wani sashi a jikin jaririn.

Don haka maganar cewa wata ta haifi Akuya ko Jaki a gaskiya wannan lamari akwai babbar ayar tambaya akai.

Dakta Hasan Abubakar ya bayar da misali inda yake cewa akwai lokaci da wani mutun ya taba zuwa dauke da cutar kaba ya sanar damu cewar cutar na damunsa amma ya sami wani mai magani ya bashi magani ya ce ya shafa a wajen da yake jin ciwon yana shafawa sai ga kadangare ya fito da nufin wannan kadangaren shine cutar kabar da ke damun sa wanda hakan ba gaskiya bane illa sharrin sihiri da wasu keyi wajen bayar da maganin gargajiya.
A Karshe dai likitan ya diga ayar tambaya akan ahaihuwar dabbar da malama Murja tayi.

Masu maganin gargajiya sun ce fa wannan lamari ko shakki hakane danAdam na iya haihuwar Dabba

Shima shahararen mai maganin nan mai suna Malam Baiwa daga Allah cewa yayi ” Wannan lamari ba abin mamaki ba ne domin kuwa karfin ikon Allah ya wuce haka.”

Malamin yayi suna wajan bayar da magani ga masu larurar ciwon Aljanu a kasa baki daya.

Sannan ya kara da cewa shi kanshi ya taba bayar da magani ga wata mai fama da kwatankwacin irin haka kuma cikin ikon Allah aka dace aka sami waraka don haka babu abin da yafi karfin Allah.
Shiko dakta Ubale mai maciji Samaru masani kan al’amuran gargajiya a kasa baki daya cewa yayi :

Tabbas Aljani kan shiga cikin jikin Bil Adama har ya haddasa masa ciwo mai tsanani don haka samun mutum ya haifi dabba ba abin mamaki bane don haka haihuwar da malama Murja tayi bai bani mamaki ba amma dai ayi kokarin kaucewa shirka da surkullen wasu mutane masu son yin kudi ko ta wani hali.
Amma bincike ya nuna cewa Dabbar da Murja tace ta haifa ba haihuwarsa tayiba kamar yadda ake haihuwa ta farji Murja ta mai bayar da magani ne ta shafata kawai sai ga Dabban ta fado.

Haka zalika malama murja ta bayyana cewa takan je asibiti don yin awo amma sai a ce mata ba a ga komai ba a cikin ta sai ruwa amma yau gashi Allah ya nuna mata ikonsa taga abin dake cikinta.

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe