27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Babban taron APC: Jerin sunayen ‘yan takarar shugaba Buhari da gwamnoni su ka sauya

LabaraiBabban taron APC: Jerin sunayen 'yan takarar shugaba Buhari da gwamnoni su ka sauya

Wasu daga cikin ‘yan takarar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke marawa baya sun sha kashi a wajen babban zaɓen jam’iyyar APC na ƙasa. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

An sauya ‘yan takarar shugaba Buhari

A wajen babban taron jam’iyyar wanda ya gudana a dandalin Eagle Square, ranar Asabar, aƙalla huɗu daga cikin ‘yan takarar da ke da goyon bayan shugaba Buhari kafin taron, aka sauya.

Sai dai sanata Abdullahi Adamu, wanda shine na farko a cikin ‘yan takarar da shugaba Buhari ya zaɓa ya samu kujerar shugabancin jam’iyyar.

‘Yan takara 6 ne su ka janye masa kafin a fara babban taron, inda Sanata Musa, ɗaya daga cikin su ya bayyana cewa mataki mai matuƙar wahala.

A wata takarda mai shafi 12 wanda aka raba a farkon taron, gwamnoni 22 na jam’iyyar sun bayyana mutum 78 domin samun kujeru a jam’iyyar.

Jerin sunayen waɗanda sauyin ya ritsa da su

Waɗanda abinda gwamnoni su ka yi ya ritsa da su sun haɗa da:

1. Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani

2. Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Adamu Aliyu

3. Injiniya Ife Oyedele

4. Architect Waziri Bulama.


Mutanen huɗu su na neman kujerun mataimakin shugaban jam’iyya (yankin kud), mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa (yankin arewa), magatardan jam’iyya na ƙasa da kuma shugaban tsare-tsare.

A madadin su, gwamnonin sun zaɓi, Chief Emma Enuekwu, Sanata Abubakar Kyari, Sanata Iyiola Omisore, da kuma Suleiman M. Argungu.

Cire mutanen guda huɗu ya tabbatar da labarin Daily Trust na ranar Laraba akan ƙulla-ƙullar da gwamnoni da wasu jiga-jigan jam’iyyar ke yi wajen tsame ‘yan takarar da shugaba Buhari ke goyon bayan su.

Babban taron APC: Wani masoyin APC ya mutu a lokacin taron jam’iyyar

Wani mai goyon bayan jam’iyya mai mulki wato All Progressive Congress (APC) ya faɗi sannan ya mutu a lokacin babban taron jam’iyyar ranar Asabar. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Ya mutu yana kan hanyar zuwa wurin taron

Magoyin bayan jam’iyyar ta APC yana kan hanyar zuwa dandalin Eagle Square, wurin da ake gudanar da babban taron, lokacin da ya faɗi ya mutu har lahira.

Wani daga cikin mutanen da ke kusa da shi ya bayyana cewa da farko yayi ƙorafin idon sa na ɗaukewa sannan ya faɗi daga baya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe