Matar da ta haifi jaki a farkon makon nan ta fara fuskantar kalubale iri-iri tun bayan aukuwar mummunan lamarin nan.
Dama sana’arta siyar da abinci don ta samu ta rufa wa kanta asiri, yaranta 11 kuma mijinta ba karfi gare shi ba.

Labarin haihuwar jakin ya yawata ko ina, har wasu suke tausaya mata suna taimaka mata, saidai a dayan bangaren, wasu sun fara kyamarta.
Wakilin LabarunHausa.com ya so tattaunawa da ita akan wannan kalubalen da ta fara fuskanta, sai dai kuma abin zai yi kama da cin fuska, hakan yasa ya tattauna da makusantanta don jin halin da take ciki.
Kamar yadda wata majiya, wacce ta bukaci a sakaya sunanta ya shaida, yanzu haka dai bata samun ciniki kamar da.
A cewarta:
“Wasu mutane sun fara kyamarta. Wasu suna ganin matsalar zata taba abincin da take siyarwa ko kuma wanda ya yi mata asirin ya yi akan kayan abincinta.
“Wannan dalilin ne yasa suka dakata da siyan abincin.”
Akwai wacce muka tattauna da ita kuma a baya kusan kullum sai ta siya abincinta, amma sai ta kada baki tace:
“Tabdijam! Jaki fa ta haifa! Ni dai gaskiya tun daga ranar da ta haifi jaki na ji ba zan samu natsuwa ba, ko da na siya abinci a wurinta.
“Saboda ina tsoron abinda zai faru da ni. Kada ya zo abinda take magana akan cewa an tura mata ya fada kan abincin da take siyarwa.”
Ta ci gaba da bayyana cewa ko wani ta ji zai siya sai ta bashi shawarar kada ya siya don gudun abinda zai kai ya dawo.
To, Allah dai yasa mu dace, ya kuma kiyaye gaba. Ameen.
Yadda na yi dakon jaki a ciki na tsawon shekaru 2, inji Talatu, matar da ta haifi jaki a Zaria
A ranar Talata, labarin Murja, wacce aka fi sani da Talatu ya bazu a cikin garin Tudun wada da ke karkashin karamar hukumar Zaria, Jihar Kaduna akan yadda ta haifi jaki, maimakon jinjiri.
Mutane da dama sun yi tunanin doki ne, sai dai da bakinta ta tabbatar wa wakilin LabarunHausa.com cewa jaki ne ba dokin ba.
Wakilin labarunHausa.com ya samu damar zuwa har gidan da ta ke zama a Layin Lemu, nan cikin Tudun Wadan Zaria, har ya tattauna da ita akan lamarin mai firgitarwa.
Kamar yadda ta bayyana, ta yadda da hakan a matsayin kaddarar ta kuma asiri ne wanda aka yi mata tun daga daukar cikin yayayyar yarinyar ta.
Kamar yadda ta shaida, bayan haihuwar diyar ta karama, kasancewar yaranta 11 a duniya, ta ke fuskantar ciwo matsananci.
A cewar Talatu:
“Na je asibitin dafta Umar inda ya duba ni bai ga komai ba. An yi min hoto amma sai likitan ya ce ruwa kadai yake gani. Magunguna dai iri-iri duk da kasancewa ta ba mai karfi ba.”
Ta shaida yadda ta samu labarin wata mata da ke Kano mai magani irin na Islamic Chemist kuma ba ta da kudi. Sai dai ta samu rance tukunna bayan matar ya zo Zaria ta duba ta har ta ce akwai ajiya a jikin ta.
Bayan yi mata addu’o’i da ba ta magunguna, sai ta haifi wannan jaririn jakin.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com