24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Neja: ‘Yan sanda sun cafke wani mai safarar kayan abinci ga ‘yan bindiga

LabaraiNeja: 'Yan sanda sun cafke wani mai safarar kayan abinci ga 'yan bindiga

Hukumar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wani Umar Dauda mai shekaru 20 wanda ya ke kai wa ‘yan bindiga abinci a jihar. Jarudar Punch ta rahoto

Ya shiga hannu bayan samun bayanan sirri

A wata sanarwa wacce kakakin hukumar, Wasiu Abiodun, ya sanya wa hannu, an cafke wanda ake zargin ne bayan samun bayanai daga mazauna garin.

An yi kamen ne a ranar 16/03/2022, da misalin ƙarfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri cewa ana yawan ganin wanda ake zargin da kai abinci da ababan sha ga ‘yan bindiga a ƙauyen Kapako cikin ƙaramar hukumar Lapai. A cewar sa

Abiodun ya bayyana cewa an tura jami’an ‘yan sanda da ke Lapai tare da haɗin guiwar ‘yan sakai zuwa ƙauyen, inda bayan dogon nazari da sa ido, su ka cafke wanda ake zargin.

An samu kayan abinci da maƙudan kuɗaɗe a hannun sa

Kakakin na ƴan sandan ya ƙara da cewa an samu kayyayakin abinci da kuɗade a hannun sa yayin binciken..

Ya bayyana cewa:

An samu waɗannan abubuwan a hannun sa; sunƙin burodi guda 6, kwalbar fearless guda 4, gwangwanin maltina 4, ɗauri huɗu na busashshen ganye da ake zargin wiwi ce, shinkafa da wake da kuma kuɗi naira miliyan 90.

Ya amsa laifin safarar abinci ga ‘yan bindiga

Abiodun ya kuma ƙara da cewa a yayin da a ke gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa yana kai wa ‘yan bindigan kayan abinci sannan su na zuwa har gidan sa a ƙauyen domin amsar kayan abincin.

Ya ƙara da cewa wannan shine karo na huɗu da wanda ake zargin ya ke safarar abinci ga ‘yan bindigan kafin ya shigo hannu.

A cewar sanarwar, a yayin gudanar da bincike, an samu bindiga ƙirar hannu a gidan wanda ake zargin.

Wanda ake zargin ya amsa cewa bindigar ta shi ce inda ya bayyana cewa ya siyo ts akan kuɗi N65,000 daga wajen wani mai haɗa bindigun a ƙauyen domin kare kan shi.

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da amarya akan hanyar kai ta gidan miji a jihar Neja

Wata sabuwar amarya ta faɗa a hannun ‘yan bindiga akan hanyar kai ta zuwa gidan mijin ta a jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta samo cewa ‘yan bindigan sun kawo harin ne lokacin da ‘yan’uwan amaryar su ka ɗauko ta daga ƙauyen Allawa a ƙaramar hukumar Shiroro zuwa garin Pandogari, a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe