24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Allah Mai Iko:Wata Budurwa mai suna Devotha da mahaifinta ya gudu ya barsu saboda kawai an haifeta da nakasa ta ginawa mahaifiyar ta gida

LabaraiAllah Mai Iko:Wata Budurwa mai suna Devotha da mahaifinta ya gudu ya barsu saboda kawai an haifeta da nakasa ta ginawa mahaifiyar ta gida
35abc59606044be6
Devotha budurwar da mahaifinta ya gudu ya barsu saboda kawai an haifeta da nakasa

Mutane na kyara da hantarar Devotha

Wata budurwa da Allah ya yi mata halittar nakasa mai suna Devotha ta gina wa mahaifiyarta gida ta hanyar amfani da kudin da ta samu a wurin wasu ayyuka da take yi. An haifi Devotha a shekara ta 1999 da kafafu a murde a baya wanda hakan ya shafi rayuwar ta, amma ta jajirce bata kashe zuciyar ta ba duk da nakasar da ke tare da ita.
A cewar Afrimax wanda sune suka tattaro tarihin rayuwar Devotha, yanayin halittar ta ya sanya mutane suke hantarar ta.
Mahaifinta ya kasance daya daga cikin mutanen da ke hantarar Devotha inda ya gudu ya bar su ita da mahaifiyar ta yaje ya kara aure.

Devotha ta na ‘yan kananan ayyukan domin samun na dogaro da kai.

Afrimax sun ba da rahoton cewa Devotha ta kasa cigaba da karatun ta saboda matsalolin kudi. Godiya ga wani Faston kauyen su, wanda ya taimata mata ta shiga makarantar fasaha inda ta sami ilimin gine-gine a sanadiyyar hakane ta yanke shawarar gina wa mahaifiyarta gida – domin ba su da gidan kan su.
Wasu daga cikin ayyuka da Devotha ke yi sun hada da wanki don tara kuɗin da ta yi amfani da su wajen siyan fili wanda ta fara ginawa da kanta.

Mahaifiyar Devotha ta cika da mamakin ‘yarta

Duk da cewa an yi rufin gidan, amma dai ba a kusa gamawa ba Amma alamarin yarinyar ya baiwa mahaifiyar ta mamaki matuka.
Ban taba tsammanin Devotha za ta iya wannnan kokarin ba” Ta shafe shekaru 8 tana gini
“Ita ce jaruma ta ce ina godiya sosai kuma ko yaushe zan kasance mai godiya,” in ji mahaifiyar Devotha.”

Devotha ta bayyana cewa ita ta yi aikin ginin da kanta. “Na siyo kwanon rufi, na samo itace da komai na gidan nan.”

Kadan daga cikin martanin Masu amfani da shafukan sada zumunta

Margie Burke ta ce: “Ina addu’a Allah Ubangiji ya albarkaci wannan budurwa da mahaifiyarta. Budurwa ce mai abin mamaki Ina roƙon Ya Ubangiji ya albarkaci wannan iyali da duk abin da suke bukata cikin sunan Yesu amin. “

Stephen Mukaabya ya ce: “Zakanya Devotha!! Babu shakka wannan abin koyi ne nakasar ki bata sa zuciyar ki mutuwa ba kin zaburar da mu gaba ɗaya! Whaaoo! Babban nasarar da ba mu lura da shi ba a tsakaninmu! Devotha ta kai kololuwar yabo masu da yawa a cikin mu baza mu iya abinda ta yi ba,! Lalle ne abin mamaki!”

Dana Ott ta ce: “Ubangiji ya albarkaci wannan yarinya ta hanyoyi da yawa.. Yayin da kowa ya shagaltu da kallon kafafunta sun rasa dukkan ni’imomin da Ubangiji ya yi mata. Tana da azama sosai. abin mamaki…✝️… Ubangiji ya kara albarka. Dukan ɗaukaka da yabo sun tabbata ga Yesu Almasihu Mai Cetonmu da Mai karɓar fansa.. Amin, Amin.”

Ina shirin siyar da motata don daukar nauyin karatun saurayina, ya cancanci hakan, Budurwa
Wata budurwa ta ba ‘yan intanet mamaki ta hanyar cewa za ta siyar da motar ta domin biyawa saurayin ta kuɗin digiri na biyu wato ‘masters’. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Budurwar za ta fara yi masa kasuwanci
Budurwar ta ƙara da cewa za ta yi amfani da ragowar kuɗin wajen fara wa saurayin na ta kasuwanci wanda a cewar ta ya cancanci komai.
Ina son na siyar da motata domin biyawa saurayi na kuɗin zangon ƙarshe domin ya samu ya kammala digirin sa na biyu.

A cewar Joy Turamuhawe
A yayin wata zantawa da TUKO.co.ke, Turamuhawe, ta bayyana cewa ita ta aminta da cuɗeni in cuɗeka.

Na ga mazaje da yawa waɗanda su ka yiwa ‘yan matan su abubuwa da dama saboda suna ƙaunar su, sannan ni na yarda da cuɗeni in cuɗeka. inji Turamuhawe.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe