24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Sama da mutum 400,000 za su gudanar da Umrah a watan Ramadan na 2022 a Saudiyya

LabaraiSama da mutum 400,000 za su gudanar da Umrah a watan Ramadan na 2022 a Saudiyya

Bayan shekaru biyu, ƙasar Saudiyya ta cire dukkanin matakan da aka sanya saboda annobar korona akan matafiya ‘yan ƙasashen waje, ciki kuwa har da allurar dole. Haka kuma matakin hana Umrah na tsawon watanni bakwai an cire shi a cikin watan Oktoban da ya gabata.

Alhazai sun yi maraba da cire matakan

Alhazawan da ke da niyyar yin Umrah a cikin watan azumin Ramadan sun ji daɗin sassauta matakan. Hakan ya nuna a yawan mutanen da ake sa ran za suyi Umrah cikin watan azumin bana, kamar yadda mataimakin ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dr. Abdulfattah Mashat ya bayyana. Ya bayyana cewa masallacin Harami zai amshi baƙuncin alhazai sama da 400,000 cikin watan azumi. Jaridar The Islamic Information ta rahoto

Ana dai buɗe Umrah ne ga matafiya ‘yan ƙasashen waje. Saudiyya ba za ta iyakance yawan ma su shigowa ba. Sai dai yawan alhazan da za su yi ibada a rana ɗaya za a iyakance shi zuwa abinda masallaci mai tsarki zai iya ɗauka domin hana cinkoso, a cewar Dr. Abdulfattah Mashat a cikin jawabin sa ga Asharq Al-Awsat.

Maƙasudin cire matakan

Mashat ya bayyana cewa tsarin cire matakan ya biyo bayan lura da yanayin annobar da aka yi a ƙasar, wanda ake samun cigaba sosai. Haka kuma yawan alluran da aka yi da kuma kayan kiwon lafiyan ƙasar ya taimaka wajen cire matakan.

Da aka tambaye shi ko nawa ne adadin alhazan da su yi aikin hajji a bana, sai ya bayar da amsa da cewa ba zaa iya sani yanzu ba duba da cewa ma’aikatar lafiya ta ƙasar har yanzu tana duba yanayin annobar.

Saudiyya ba za ta iyakance yawan alhazan da za ta amsa ba

Ya kuma ƙara jaddada cewa Saudiyya ba ta sanya adadin yawan alhazan da za ta ƙarba ba. Ƙasar za ta amshi dukkanin wanda samu iznin yin Umrah.

Gidajen cin abinci ba za su sayar da abinci ba a lokacin azumin watan Ramadana, In ji hukumar Saudiyya

Hukumomin Saudiyya har yanzu sun hana gidajen abinci sayar da abinci a lokacin azumin watan Ramadan.

Wata wasiƙa da aka yaɗa a yanar gizo kwanan nan ta haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta. Ta yi iƙirarin cewa za a bar gidajen abinci a Saudi Arabiya su yi abinci a lokacin azumin Ramadan na wannan shekara. A cewar wasikar, gidajen cin abinci za su iya ci gaba da sayar da abinci ga baƙi ko masu yawon bude ido muddin sun sanya labule ko kuma rufewa

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe