24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Gaggawa: Wani mutumi ya bayyana cewar ana saurin binne gawa tun da sauran numfashi kamar yadda aka kusa yiwa Dansa

LabaraiAl'adaGaggawa: Wani mutumi ya bayyana cewar ana saurin binne gawa tun da sauran numfashi kamar yadda aka kusa yiwa Dansa
gawa
Ana saurin binne gawa tun da sauran numfashi

Da yawan mutane a kabarin su suke karasawa

Wani mutumi a jihar Kano, mai suna Nura Ahmad Mahmud ya ce, gaggawar da mutane ke yi wajen kai gawa kushewa da ga zarar an ga numfashin mutum ya dauke, hakan ne ke sanyawa a rufe wasu da sauran numfashin su.

Ya bayyanawa majiya yadda aka kusa rufe dansa da rai

Mutumin, ya bayyana hakan ne, a wata zantawa da akayi dashi a gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Alhamis.
Inda ya kara da cewa “Ni kaina irin wannan al’amarin ya taba faruwa da dana, an fada mana cewar ya mutu, amma saboda jinkiri da mu ka yi wajen shirya shi don kaishi kushewa, hakan ne ya ceto rayuwar yaron,yanzu haka yaron yana nan yana ci gaba da rayuwa yana yawon sa ko ina”.

Mutumin ya kara da cewa “ shekarar mu ashirin, Allah bai azirtamu da haihuwa ba, kwatsam ta samu ciki,ranar da ta haihu, sai likitoci su ka shaida mana cewar, jaririn fa ba zo da rai ba, ba muyi gaggawar kaishi makabar ta ba , jim kadan sai muka lura kafafunsa na motsi”. A cewar Nura Ahmad
Nura Ahmad Mahmud, ya shawarci al’umma, da su rinka jinkirta binne ‘yanuwan su zuwa wani lokaci, domin gujewa binne gawa da rai.


Wani dalibin Yukirain dan Najeriya ya mutu a sakkwato, sati biyu kacal bayan an tseratar dasu

Wani dalibi dan Najeriya mai suna Uzaifa Halilu Modachi, da yake karatu a kasar Yukirain ya mutu, a garin Sokoto, sati biyu kacal bayan dawowar sa Najeriya.

Kafin rasuwar sa Halilu Modachin, ya zauna a kasar Yukirain din tsawon shekara uku ba tare da ya dawo hutu gida Najeriya ba.
Dan shekarar karshe a karatun sa, a jami’ar lafiya ta Zaporozhye, yana kan shirin fara jarrabawar karshe ne yaki ya barke tsakanin Yukirain din da kasar Rasha.
Da yake bayyana alhininsa, baban mamacin honarabul Habibu Haliru Modachi, dan majalisa a jihar Sokoto, yace :

” Alhandulillah, Allah shine ya bayar da rayuwa , kuma ya karbi abarsa, haka ya tsara abin sa kuma bamu da ja akan hakan”

“Da ace a kasar Yukirain ya rasu, sai an fadi abubuwa da yawa akan sa, ko ace sojojin Rasha ne suka kashe shi, ko ace yayi hadari, ko kuma ace sojin Yukirain ne suka harbe shi.

” Muna matukar godiya ga Allah da ya sanya ya mutu a gabanmu, muna kuma matukar godiya ga gwamnati, musamman ta jihar Sokoto, saboda kokarin tseratar dasu da tayi tun kafin rincabewar yakin na Yukirain.

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe