24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Ina shirin siyar da motata don daukar nauyin karatun saurayina, ya cancanci hakan, Budurwa

LabaraiIna shirin siyar da motata don daukar nauyin karatun saurayina, ya cancanci hakan, Budurwa

Wata budurwa ta ba ‘yan intanet mamaki ta hanyar cewa za ta siyar da motar ta domin biyawa saurayin ta kuɗin digiri na biyu wato ‘masters’. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Budurwar za ta fara yi masa kasuwanci

Budurwar ta ƙara da cewa za ta yi amfani da ragowar kuɗin wajen fara wa saurayin na ta kasuwanci wanda a cewar ta ya cancanci komai.

Ina son na siyar da motata domin biyawa saurayi na kuɗin zangon ƙarshe domin ya samu ya kammala digirin sa na biyu.

A cewar Joy Turamuhawe

A yayin wata zantawa da TUKO.co.ke, Turamuhawe, ta bayyana cewa ita ta aminta da cuɗeni in cuɗeka.

Na ga mazaje da yawa waɗanda su ka yiwa ‘yan matan su abubuwa da dama saboda suna ƙaunar su, sannan ni na yarda da cuɗeni in cuɗeka. inji Turamuhawe.

Ina son na siyar da motata domin biyawa saurayi na kuɗin zangon ƙarshe domin ya samu ya kammala digirin sa na biyu. Ina tunanin zan yi amfani dansairan kuɗin wajen fara masa ƙaramin kasuwanci yayin da ya ke neman aiki tunda yana son yayi abinda ya karanta. Matashin sarki ya cancanci komai.

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

Bayan ta yi wannan wallafar a shafin Twitter, ga abinda mutane ke cewa:

Joansheenah ya ce:

Cikin hawaye abin zai ƙare.

Brökë_C3lëbrïty ya ce:

Idan har da gaske ne to ina so na zama saurayin ki. Ina mamaki yadda wani ya ke ƙoƙarin neman digiri na biyu amma bai da aikin yi.

Marvin k ya ce:

Gaskiya ka da ki siyar da motar ki. Idan zai yiwu ki amshi bashi, sannan ki yi amfani da motar ki a matsayin jingina, kowane banki zai baki bashin kuɗi daganan sai ki dinga biya a hankali a hankali, saboda za ki buƙaci motarki sannan saurayin ki yayi sa’ar samun ki.

Bidiyon budurwa tana rusa kuka akan saurayinta da suka yi shekaru 6 tare ya bar ta zai auri zabin mahaifiyar sa

Wata budurwa ta shiga cikin matsanancin tashin hankali kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo tana rusa kuka.

A wani bidiyon TikTok wanda shafin LIBsuka wallafa an ga budurwar cike da kunci har tana bayyana cewa shekarun su 6 tare da saurayin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe