35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Kotu ta yi watsi da ƙudirin gwamnatin Faransa na rufe wani masallaci

LabaraiKotu ta yi watsi da ƙudirin gwamnatin Faransa na rufe wani masallaci

Wata kotun kasar Faransa ta rushe kudirin gwamnatin kasar na rufe wani masallaci da ke a birnin Bordeaux. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Lauyan kungiyar masallacin Al Farouk, Sefen Guez Guez, a ranar Laraba ya ce kotun Bordeaux Administrative ta yi watsi da kudirin gwamnatin na ranar 14 ga watan Maris na rufe masallacin har tsawon watanni 6.

Anyi maraba da hukuncin

Ya lurar da cewa hukuncin kotun wani babban cigaba ne akan yadda gwamnati ta ke rufe masallatai ba bisa ƙa’ida ba. Ya kara da cewa masallacin yana zama a matsayin wurin haɗuwar musulmai.

An rufe masallacin Al Farouk da ke yankin Pessac kusa da garin Bordeaux bisa zargin shi da kare musuluncin tsageranci da kuma yada akidar salafanci.

Faransa
Kotu ta yi watsi da ƙudirin gwamnatin Faransa na rufe wani masallaci. Hoto daga Jaridar Daily Trust.

A watan Augusta, hukuma mafi karfi ta kundin tsarin mulkin Faransa ta amince da wata doka mai cike da ruɗani wacce aka dinga caccaka kan nuna wariya ga musulmai.

Majalisar dokokin ƙasar ta Amince da dokar a watan Yuli duk da yadda wasu daga cikin ‘yan majalisar su ka nuna adawa da dokar.

Gwamnati ta yi iƙirarin cewa maƙasudin dokar shine ƙara ƙarfafa “addinin Faransa” sai dai ma su sukar dokar su na ganin cewa dokar ta tauye haƙƙin gudanar da addini ga musulmai sannan ta ware su.

An soki gwamnatin Faransa akan dokar

An dinga caccakar dokar akan kai hari ga al’ummar musulman Faransa, wadanda su ne suka fi yawa a nahiyar Turai, inda su ke da mabiya miliyan 3.35, sannan da kuma hana walwala na harkokin rayuwarsu na yau da kullum.

Dokar ta bai wa jami’ai damar shiga harkokin masallatai da ƙungiyoyin su wajen gudanarwa tare da lura da iko akan harkokin kudaden ƙungiyoyin musulmai da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Har ila yau, dokar ta taƙaita wa musulmai damar zabar darussan koyawa a gida har sai an samu amincewar jami’ai. Sannan kuma a ƙarƙashin dokar, an haramta wa marasa lafiya damar zabar jinsi ko addinin likitan da zai duba su.

Tun a watan Fabrairun shekarar 2018, ƙasar Faransa ta dade tana ƙarbe ikon masallatai 25,000, makarantu, ƙungiyoyi da masana’antu. Kuma ta rufe guda 718, ciki har da masallatai 20, kamar yadda wani rahoton da aka wallafa a 2 ga watan Maris ya nuna.

Ƙasar Faransa ta kafa wata sabuwar hukuma wacce za ta sauya fasalin addinin Musulunci a fadin kasar

Ɗumbin musulmai ma su faɗa aji a ƙasar Faransa, gwamnati ta zaɓo domin kasancewa cikin taron kafa hukumar musulunci. Waɗanda ke sukar lamarin na ganin cewa wannan wani yunƙurin shugaba Emmanuel Macron ne na samun goyon baya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe