27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Budurwa ‘yar Najeriya ta tsere da N140,000 da POS ranar da ta fara aiki, ta yi amfani da bayanan ƙarya akan CV

LabaraiNajeriyaBudurwa ‘yar Najeriya ta tsere da N140,000 da POS ranar da ta fara aiki, ta yi amfani da bayanan ƙarya akan CV

Wani dan Najeriya mai suna @Letter_to_Jack, ya ɗauki wata ma’aikaciya Ashiru Dupe Adedayo, wanda rahotanni suka nuna ta gudu da kuɗi har N140,000 a ranar da ta fara aiki.

Matar ta kwashi kuɗin ne a ranar farko da ta fara aiki bayan ta bayar da bayanan karya a kan CV din ta
‘Yan Najeriya da dama sun nemi @Letter_to_Jack ya isar da sakonsa a Facebook don samun babbar yuwuwar gano ta.

Lady Abscond
Budurwa ‘yar Najeriya ta tsere da N140,000 da POS ranar da ta fara aiki, ta yi amfani da bayanan ƙarya akan CV

Wani dan Najeriya da aka fi sani da @Letter_to_Jack a shafin Twitter a ranar Laraba, 23 ga watan Maris, ya shiga dandalin don yin cikakken bayani kan wata mata, Ashiru Dupe Adedayo, wacce ta gudu da kudin ubangidanta.

A cewarsa, a ranar farko da ta fara aiki, an baiwa Dupe kudi naira 100,000 tare da na’urar POS mai dauke da Naira 40,000. Mutane sun shiga Facebook don tono hotunanta. Lambar da za a kira idan an same ta @Letter_to_Jack wanda shi ma ya raba hoton matar ya ce duk bayanan da ke kan CV na ma’aikaciyar an gano na bogi ne.

Shagon POS din yana Fagba, tashar Bus ta Iju, karamar hukumar Ifako Ijaiye. Ya buƙaci mutane su kira +2348147724954 idan sun ga matar.
Mutane da yawa sun raba hotunanta da suka samu daga Facebook. Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin ra’ayoyin na su kamar haka:


@alienstrange ya ce: “Fagba ke, sa na nuna wa yaran obawole hotonta kila sun san ta.”
@SegunOladejo_ ya ce: “Zakuyi mamakin abinda zatayi amfani da kudin.”
@SoulXtra100 ya ce: “Na kasance a Ifako Ijaiye jiya don binne kakar wata kawarta, ina tsammanin nayi amfani da POS dinta.”

@Lanredeola ya ce: “Babu wani bayani da aka tabbatar kafin a yi mata aiki? Abu ya girmama. Ta yaya ma ka san ainihin sunanta kenan? Yanzu ka sai ka nemi NIN ka yi tabbaci kafin ka ɗauki wani .”

@MISTER_PANACHE ya tambaya: “Idan duk abin da ke cikin CV ɗinta na karya ne, ta yaya za ku san wannan shine ainihin sunanta?”
@tajudine2013gm2 said: “Ku ba su aiki, na gaba su yi sata. Amma su irin wadannan za su yi kukan rashin aikin yi, rashin amana wata babbar matsala ce ga sabbin saka hannun jari a kasar .”

Makaho ɗan Najeriya mai shekaru 44 wanda baiyi jami’a ba ya kera wayoyin hannu 2, yana neman haɗin gwiwa

Wani dan Najeriya mai fama da matsalar gani mai suna John Msughter ya ƙera wata wayar salula mai suna Chelsea Mobile Mate 40 Pro, Chelsea Mobile Mate wadanda ba sune wayoyi John na farko ba kamar yadda ya Ƙirƙiri wata waya a shekarar 2018.

Fasihin mai shekaru 44 da haihuwa wanda ba shi da ilimin jami’a ya riga ya ba da izinin a yi amfani da ƙirƙirar sa kuma yana neman haɗin gwiwa don samar dasu.

John Msughter na ɗaya daga cikin ɗimbin matasan Najeriya da ke baje-kolin hazaƙa da ke da yawa a ƙasar.

Mutumin mai shekaru 44, duk da cewa yana da nakasa, ya ƙera wata wayar salula da ya kira Chelsea Mobile Mate 40 Pro duk da cewa bai samu ilimin jami’a ba. John ya fara ƙera waya mai suna Chelsea Mobile K7 a cikin 2018

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe