22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Dakyar nasha yafi dakyar aka kamani:Tsananin tsoron duka yasa wani yaro dalewa jikin gini kamar ‘spiderman’

LabaraiDakyar nasha yafi dakyar aka kamani:Tsananin tsoron duka yasa wani yaro dalewa jikin gini kamar 'spiderman'
b95db844609b8459
Tsananin tsoron duka yasa wani yaro dalewa sama kamar’ spider man’

Gudun ceton rai

In kaga mutuwa a fili zaka aikata komai don ceton rai, Hakan ne ta faru da wani ƙaramin yaro a lokacin da yake fuskantar ‘ horo a gida. Yaron ya lailaye mahaifiyar sa ta hanyar dalewa jikin gini kamar ‘spiderman’ saboda gujewa dukan da take masa.

Da ya tsaya a jibgeshi gara ya haye sama

A cikin wani faifan bidiyo da @chemicalbrodar ya wallafa a shafin Twitter,an hangi mahaifiyar yaron rike da zanin ta dayan hannun kuma rike da silifas inda take kokarin kwadawa yaron.
Yaron makale a saman bango, daga mahaifiyar ta yi kokarin isa gareshi sai ya kara hayewa sama.
Ga kadan daga cikin Martanin masu amfani da shafukan sada zumunta

@purest_toyin ya ce: “Idan Mahaifiyata ce cewa zatayi in cigaba da makalewa a saman har sai sanda Allah ya kawo bakon ido kila ta amince in sauka.”

@rossyflower1 ta ce: “a tunanina da ta hakura ya sauko. Kasancewar sa a wurin akwai hadari babba duk da ya dale saman bata hakura ba tana kokari dukan sa”

@stormzo2_photography ya ce: “Wasu Yaran zasu sa mutun ya yi hauka……….. Abin ban dariya, idan wannan yaron ya girma, zai dinga tuna wannan abin dariya….. kowa ya yi wannan yarantar…. gara ma ka sauko ka amshi rabon ka….Mama ta sa hulan kwano…”

@3plejaay ya ce: “Ba ka ga komai ba, iyayen 1980s neman abin zama zatayi ta jira har sai gabobinka sun yi tsami da ga nan za ka gane bambanci tsakanin karya da gaskiya saboda chanza abin duka zata yi daga silifas zuwa bulaliyar fatun akuya, robar tiyo kore da baki ko ja da baki a takaice dai ka mutu a saman kawai.”

Miji,mata da ‘yayansu sun tsallake rijiya da baya,yayinda fankar sama ta rufto musu

Wata mata ‘yar Najeriya mai suna Yvonne Stanley ta ba da labarin yadda ita da iyalanta suka tsallake rijiya da baya. A wani sakon da ta wallafa a Facebook a ranar Laraba, 23 ga watan Maris, ta bayyana cewa fankar su ta fado kan gado a daidai lokacin da ita da mijinta su ke shirin kwanciya.
Yvonne ta kasa daina mamakin wannan al’amari cikin ikon Allah fankan ta rufto ba tare da taba yaran ta da ke kwance a kan gado ba duk da ‘ yadda su ka baje suna kwasar baccin su.’
Ta kara da cewa fankan ya fado ne a dai dai wurin da suka saba zama ita da maigidanta,abin da ya,hana fankar fadowa kansu ba su zauna a wurin ba ne a wannan lokacin. Abinda ta ce kamar haka:

“Ba zan iya yin shuru ba game da wannan lamari ba ooooo… Da yanzu ‘yaya na sun zama marigaya,da rudewan yafi haka.
Ina jin labarin yadda ake samun asaran rayuka a hadarin fanka, babu wanda ya yi tsammanin haka.
A daren jiya da misalin karfe 11:15 na dare, a gaban idan mu ni da mijina fankar sama tana tsaka da aiki ta rufto kasa ba tare da wani sauti ko alama ba.
“Yadda Allah ya tsare wadanna yaran ya tura su gefe guda duk da “yadda suke bajewa in suna bacci”. Ya kara tsaremu ni da mijina ba mu zauna wurin da muka saba zama ba. Allah ya kaddara kaifin fankar nan ba zai cutar da mu ba.
“Dubi irin yadda su ke juyi dai dai lokacin da na dauki wannan hoton. Mai kake ganin zai faru in da fankar ta fado a kansu. Da kafar su zata gutsire “me Idan“…”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe