24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Kano: ‘Yan sanda sun cafke wasu ƙananan yara bisa halaka wata matar aure saboda wayar salula

LabaraiKano: 'Yan sanda sun cafke wasu ƙananan yara bisa halaka wata matar aure saboda wayar salula

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wani yaro mai shekaru 18, Abdulsamad Suleiman, wanda ke zaune a Dorayi Chiranchi Quarters, Gwale, cikin birnin Kano, tare da abokin harƙallar sa Mu’azzam Lawan, mai shekaru 17, bisa zargin hallaka wata matar aure. Jaridar Punch ta rahoto

Kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar SP Abdullahi Haruna, a cikin wata sanarwa ranar Alhamis ya bayyana cewa:

‘’A ranar 12 ga watan Fabrairun 2022, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, mun karɓi rahoto daga wani mazaunin Danbare Quarters, ƙaramar hukumar Kumbotso, ta jihar Kano, cewa a wannan ranar da misalin ƙarfe 8 na dare bayan ya dawo gida daga wajen aikin sa, ya samu matarsa Rukayya Jamilu mai shekaru 21, kwance cikin jini. Ba ta iya motsi akan gadon ta tare da yaranta guda 3, Amina, Jamilu da kuma wani cikin munanan raunika.

'Yan sanda
Kano: ‘Yan sanda sun cafke wasu ƙananan yara bisa halaka wata matar aure saboda wayar salula. Hoto daga jaridar Punch

An tura jami’an ‘yan sanda

A cewar sanarwar, bayan karɓar rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sama’ila Dikko, ya tura tawagar jami’ai bisa jagorancin DPO, SP Ibrahim Hamma, zuwa inda lamarin ya auku.

Bayan sun isa, tawagar ta garzaya da waɗanda abin ya ritsa da su zuwa asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda aka tabbatar da mutuwar matar auren, yayin da ake cigaba da kula da sauran mutum biyun.

Binciken da sashin masu binciken laifuka na hukumar ya gudanar tare da jami’an DSS ya sanya an cafke babban wanda ake zargi,  Abdulsamad Suleiman, mai shekaru 18, wanda ke zaune a Dorayi Chiranchi Quarters, ƙaramar hukumar Gwale, jihar Kano, tare da abokin harƙallar sa, Mu’azzam Lawan, mai shekaru 17, wanda su ke zama tare a wuri ɗaya.

Wanda ake zargin ya amsa laifin sa

Kakakin hukumar ta ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa bayan gudanar bincike, babban wanda ake zargin ya amsa cewa a ranar 12 ga watan Fabrairun 2022, da misalin ƙarfe 4 na yamma, yaje gidan mamaciyar inda ya tarar da ita akan gado.

Haruna ya ce:

Bayan wanda ake zargin ya gaishe ta, ya ga wayoyi guda uku sannan ya ɗauke su. Bayan ya fahimci cewa matar auren za ta gane shi, yayi amfani da taɓarya inda yayi ta kwada mata a kai, sannan kuma ya doke yaranta guda biyu kafin ya gudu da wayoyin.

Haka kuma, wanda ake zargin ya amsa cewa, ya bayar da ɗaya daga cikin wayoyin ga abokin shi sannan ya siyar da sauran guda biyun akan kuɗi N12,000, kamar yadda abokin harƙallar ta sa ya amsa cewa ya siyar da wayar da aka bashi akan kuɗi N2,000.”

Bayan kammala bincike, sanarwa ta yi nuni da cewa za a miƙa lamarin zuwa kotu.

Kano: Yadda kotu ta sakaya Ado a gidan yari akan satar dunkulen Maggi

Wata kotu da ke zama a Jihar Kano ta sakaya wani mutum mai shekaru 37 a gidan gyaran hali akan satar katan din dunkulen maggi, LIB ta ruwaito.

Wanda ake zargin, Yusha’u Ado, mazaunin Goron Dutse Quarters ne da ke Kano, kuma yanzu haka ana zargin sa da cin amana tare da cuta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe