35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ruwan Sharhi : Yayin da wani kyakkawan rubutun hannu na shugaban kasa Buhari ya karade yanar gizo

LabaraiRuwan Sharhi : Yayin da wani kyakkawan rubutun hannu na shugaban kasa Buhari ya karade yanar gizo

Joe Igbkwe, babban dogarin gwamna, Bankside Sanwo-Olu, ya bayyana wani kyakkyawan rubutun hannu, na Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata 22 ga watan Maris, wanda ya rubuta a yayin kaddamar da bude masana’ntar takin zamani ta Dangote a unguwar Lekki dake jihar Legas . 


Shugaba Buharin ya rubuta wani jawabi, bayan kaddamar da katafaren aikin da ya lashe biliyoyin daloli, wanda babu tantama zai kawo gagarumin sauyi ga tattalin arzikin Najeriya. 

A sakon da ya rubuta, shugaban kasar yace, gagarumin aikin, ya dace da manufar gwamnatin sa na taba rayuwar mutane da dama ta fuskar bunkasa tattalin arziki, musamman ma manoma.

rubutun buhari
Ruwan Sharhi : Yayin da wani kyakkawan rubutun hannu na shugaban kasa Buhari ya karade yanar gizo


Ya kara da cewa,  kaddamar da katafariyar masana’ntar ya kara tabbatarda fatan samun yan kasa masu arzikin masana’ntu, abune mai yiwuwa a Najeriya.


Takaitaccen sakon da aka rubuta shi da yadda zai iya karantuwa, amma a cikin salo irin na malkwasa mai ban kaye, yana cewa : 

“Kamfanin Dangote na takin zamani da na kaddamar yayi daidai da manufar gwamnatin mu ta canja rayuwar manoma, da bunkasa tattalin arzikin su da kuma adana darajar kudaden kasar waje na kasa.” 


“Wannan taro na yau a Ijebu dake Lekki, tabbacine na cewa babu wani abu da zai zama wahala ga yan kasa masu hangen nesa gami da burin kafa manyan masana’ntu kamar su Dangote.

 “Ina tayaka murna”

Sharhin yan Najeriya akan rubutun

Yan Najeriya da yawa sunyi sharhi akan sakon Igbokwe din da mabambantan ra’ayoyi da fahimta. 
Amma wadansu mutanen, suna kallon shugaban kasar a matsayin mai dattako, ta yadda bazai yi karya ba da wani rubutun hannu. 

Ga sharhin  mutane na Facebook : 

Amb Kuseme

“Idan har zai iya irin wannan rubutun, me yasa yake tafi da kasar ta wannan hanyar?, ko dai akwai wani abu da bamu sani ba, ina tambaya ne a madadin yan uwanmu dake yankin kabilar Igbo “

Arome Attah: 

” Babu wuta, babu mai babu kyakkyawan shugabanci, rubutun hannun waye zai dame mu, ehh?, na waye? “

Samuel Omolola Edema :

” Hmmm ina tunanin yana so yace ne… Babu abin da ba zai yiwu ba ga shugabanni masu fata… Amma sai yace,…  Babu abin da ba zai yiwu ba ga yan kasa masu fata irin su Dangote… “

Segun Fagbemi: 

“Wannan shine rubutun tsoho dan shekara 80, kai amma fa yayi kyau.”

Mai rubutun adon Kiswa na Ka’aba Rajab Mahoos ya rasu bayan hidima ta shekara 47

Dan asalin kasar Saudi Arabia mai suna Rajab Mahoos Al maliki, daya daga cikin manyan masu yin kwalliyar zinare na dakin ka’aba, ya rasu bayan ya shafe shekara 47 yana hidimar dakin Ka’aba. 


A Saudi Arabia akwai wani birnin na musamman da aka ware domin yin ado ga dakin ka’aba  wanda aka fi sani da Kiswa. 

Yadda mamacin ya dauki Kiswa da mahimmanci


Mamacin ba kawai rayuwar sa ya bayar ga hidimar Kiswa ga dakin Ka’abar ba, a’a aikinsa yana yinsa cikin karsashi da nishadi da kuma salo. 

Ya rasu yana dan shekara casa’in a wani asibitin kudi. Yayi murabus daga aikinsa tun shekarar 2004. Amma duk tsawon rayuwar sa ya tafiyar da ita wajen bada gudummawar yadda ake yin Kiswa din wato adon zinare ga dakin na Ka’aba. 
Haka kuma, ya kasance yana jin wadata da  wannan aikin nasa mai kima. 

Inda mai adon Ka’abar ya rasu


A duk inda ake taron jama’a kuma ya zamto zai fadi wani abu, to zai mike ya fadi cewa shi mai aikin Kiswa ne na Ka’aba, sannan yana kokarin nuna wani karin haske a kan aikin. 

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe