24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Uwargida ta hau kujerar naki ta ki amincewa da mijinta har sai an yiwa amarya gwajin cuta mai karya garkuwan jiki

LabaraiUwargida ta hau kujerar naki ta ki amincewa da mijinta har sai an yiwa amarya gwajin cuta mai karya garkuwan jiki
images 58 2
uwargida ta hau kujerar naki taki amincewa da mijin ta har sai anyi wa amarya gwajin cuta mai karya garkuwan jiki

Uwargida ta ce sam bata aminta da amaryar mijin ta ba har sai anyi gwaji

Wata uwar gida a garin Kano, ta ki amincewa da mijinta saboda ta na zargin ya auro amarya ba tare da an yi gwajin cuta mai karya garkuwan jiki ba.

Tuni Uwar gidan ta garzaya wurin hukumar Hisba da ke jihar Kano inda ta kai kukanta, ita kuma hukumar Hisab batayi kasa a gwiwa ba ta gayyato ma’auratan,inda aka yi musu gwaji, sai dai har yanzu hukumar ta Hisba ba ta bayyana sakamakon gwajin ba.

Ga cikakken rahoto a muryar da ke kasa.

Tsohuwar jarumar Kannywood Naja’atu Muhammad, wacce ta yi fim din Murjanatu ‘yar Baba ta haihu


Aure ya yi albarka, tsohuwar jarumar Kannywood, Naja’atu Muhammad wacce aka fi sani da Murjanatu ‘Yar Baba ta haihu yau, ranar Alhamis, 24 ga watarin Maris din shekarar 2022.
Kamar yadda ya bayyana, ta haifi yaro namiji yau da safen nan kuma tana cikin koshin lafiya.

Bayan wallafar ta shi, nan da nan mutane suka fara wallafawa a shafukansu, fitatattun shafuka kamar Arewafamilyweddings ma sun wallafa.

Manyan jarumai da mawaka, kamar Ali Nuhu, Ali Jita da sauran su sun bazama wurin yi masa barka suna fatan Allah ya raya.

Kamar yadda ya wallafa da harshen turanci:
Muna farin cikin sanar da ku cewa mun samu karuwar da namiji. Mahaifiyarsa da yaron duk suna cikin koshin lafiya. Mun gode wa Allah.

“Muna farin cikin zuwan jaririn mu yau da safe. Mun gode da addu’o’in ku.”

Tun bayan fim din da jarumar ta yi a lokacin tana karama, Murjanatu ‘Yar Baba, ta samu daukaka da kuma suna.

Mutane da dama sun yi tunanin zata ci gaba da fim idan ta girma. A baya an ga yadda take kawance da Jaruma Maryam Yahaya sosai, bayan bayyanar ta a bikin birthday din ta.

Sai dai an ji ta shiru. Ko a Instagram sai dai a dinga ganin hotunanta jefi-jefi.

Mijin ta, fitaccen dan kwallon kafa ne, kuma matashi mai kananun shekaru. Yanzu haka majiyoyi sun nuna cewa ba sa rayuwa a Najeriya, suna kasar Turkiyya.

Da alamu suna yin rayuwarsu ne cike da sirri saboda wasu dalilai da suka bar wa junayensu. Don ko daurin aurensu a rurrufe aka yi.

Tun bayan auren, bata fiye wallafa hotunanta ba, sai dai mijin ne wani lokacin yake wallafa hotunansu tare.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe