29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wata ‘yar aikin gida ta bar aiki cikin gadara da jiji da kai, bayan wata 5 kuma ta dawo tana magiya a mayar da ita

LabaraiWata 'yar aikin gida ta bar aiki cikin gadara da jiji da kai, bayan wata 5 kuma ta dawo tana magiya a mayar da ita

Mai gabatar da shirin rediyo Cynthia Anyango, ta jadda wani darasin rayuwa, cewa ko wacce uwa tana fama da yau da gobe. 

A fadar ta, wata yar aikin gida ce wadda ta bar gurin aikin ta, tana mai matukar girman kai da jiji da kai, yanzu ta dawo tana magiya a mayar da ita. 

Anyango din, ta kara da cewa, koda an tausaya mata domin a mai da ita, to bakin cikin da ta kuntuka na rashin nuna da’a bazai bari ba. 

Wata mai gabatar da shirin rediyo a gidan rediyon kasar Kenya, Cynthia Anyango, ta bayyana wana wata mata da ta taba yi mata aikin gida, yanzu ta dawo tana yi mata magiya domin ta mayar da ita. 


A wani sakon yanar gizo, Anyango din ta bayyana cewa mai aikin tata ta bar aiki a watan Oktoban shekarar da ta gabata, cikin nuna girman kai da dagawa. 

yar aiki
Wata ‘yar aikin gida ta bar aiki cikin gadara da jiji da kai, bayan wata 5 kuma ta dawo tana magiya a mayar da ita


Ta bar aikin ne cikin tsakar dare h

A fadar ta, koda yake tare suka wani a gidan ita da yar aikin nata, amma bata gaya mata ta bar aikin ba sai cikin tsakar dare. 


“Abin da ya fi komai ciwo, shine ta sani sarai ce ina tashi da karfe ukun dare 3 domin na tsara shirina na sutudiyo, ” ta bayyana 

Abin da ya bata haushi da ‘yar aikin


Anyango tace babban abin haushin kuma shine, ta kai tsawon shekara 3 muna tare. Tace Allah ne kadai ya san irin kulawar da ta bata tsawon zaman su. 

Kinga babu gurbin wani aiki !


Bayan ta ce ta bar aikin Anyango tace, zata iya tunawa, yadda cikin gadara yar aikin tace mata :

“sai nema wata yar aikin daga ofis” 


“Wanda haka naji yayi wani banbarakwai, tunda itama ba daga ofis na nemo ta ba. Hakan yayi mini ciwo kwarai, amma sai na dance, saboda ba girmana bane na biye mata “. Ya bayyana 


Anyango tace tayi matukar mamaki da ta daga wayar ta taga wai ana rokonta da magiya wai ta dawo da yar aikin nata kan aikin ta. 


Tambaya daya kawai Anyango tayi wa mai kiran cewa, da tana tunanin wai dan ta bar aiki a karkashin ta, aikin gidanta zai tsaya ne cik har sai sanda ta dawo? 


“Abin da na daya mata kawai shine ni yanzu ina da yar aiki, kuma bana bukatar aikin ta. Abin da ya tafi ne kuma wai yanzu ya dawo”.

BASAJAN AIKI: Bayan wata uku 3, wata mata ta gano ‘yar aikin da ta dauka ba mace bace, gardi ne 

Wata mata ‘yar Nageriyar ta dauki wata ‘yar aiki, bayan wata uku sai ta gane ashe burum-burum ‘yar aikin tayi mata. 
Matar ta gano cewa ‘yar aikin dai ba mace bace namiji ne inda ta kunyata shi a cikin bidiyon da ya dinga kewayawa a kafafen sada zumuntar zamani.

Anyi ta samun ra’ayoyi mabanbanta juna lokacin da bidiyon dan basajan aikin ya yadu, inda mutumin ya zamo abin ya taba shi sosai. 

Kaddara cewa ku dauki yar aiki mace, bayan wani lokaci kuma ku gano cewa wannan ‘yar aikin ba mace bace namiji ne. Wannan shi ne abin da ya faru da wata magidanciya. 

Matar wacce babu wani takamaiman bayani a kan wacece ita, ta ga abinda ta kasa yarda da shi, cewa mai aikin gidanta ba mace bace namiji ne. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: NAN

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@alamfas

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe