24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Tsohuwar jarumar Kannywood Naja’atu Muhammad, wacce ta yi fim din Murjanatu ‘yar Baba ta haihu

LabaraiKannywoodTsohuwar jarumar Kannywood Naja'atu Muhammad, wacce ta yi fim din Murjanatu ‘yar Baba ta haihu

Aure ya yi albarka, tsohuwar jarumar Kannywood, Naja’atu Muhammad wacce aka fi sani da Murjanatu ‘Yar Baba ta haihu yau, ranar Alhamis, 24 ga watarin Maris din shekarar 2022.

Mijinta, Abdullahi Shehu, fitaccen dan wasan kwallon kafa ne, ya wallafa hakan a shafin sa na Instagram.

yar baba
Tsohuwar jarumar Kannywood Naja’atu Muhammad, wacce ta yi fim din Murjanatu ‘yar Baba ta haihu

Kamar yadda ya bayyana, ta haifi yaro namiji yau da safen nan kuma tana cikin koshin lafiya.

Bayan wallafar ta shi, nan da nan mutane suka fara wallafawa a shafukansu, fitatattun shafuka kamar Arewafamilyweddings ma sun wallafa.

Manyan jarumai da mawaka, kamar Ali Nuhu, Ali Jita da sauran su sun bazama wurin yi masa barka suna fatan Allah ya raya.

Kamar yadda ya wallafa da harshen turanci:

“Muna farin cikin sanar da ku cewa mun samu karuwar da namiji. Mahaifiyarsa da yaron duk suna cikin koshin lafiya. Mun gode wa Allah.

“Muna farin cikin zuwan jaririn mu yau da safe. Mun gode da addu’o’in ku.”

Tun bayan fim din da jarumar ta yi a lokacin tana karama, Murjanatu ‘Yar Baba, ta samu daukaka da kuma suna.

Mutane da dama sun yi tunanin zata ci gaba da fim idan ta girma. A baya an ga yadda take kawance da Jaruma Maryam Yahaya sosai, bayan bayyanar ta a bikin birthday din ta.

Sai dai an ji ta shiru. Ko a Instagram sai dai a dinga ganin hotunanta jefi-jefi.

Mijin ta, fitaccen dan kwallon kafa ne, kuma matashi mai kananun shekaru. Yanzu haka majiyoyi sun nuna cewa ba sa rayuwa a Najeriya, suna kasar Turkiyya.

Da alamu suna yin rayuwarsu ne cike da sirri saboda wasu dalilai da suka bar wa junayensu. Don ko daurin aurensu a rurrufe aka yi.

Tun bayan auren, bata fiye wallafa hotunanta ba, sai dai mijin ne wani lokacin yake wallafa hotunansu tare.

Yanzu haka in banda wallafar da mijinta ya yi, babu wanda yasan tana da juna biyu balle ta haihu.

Muna fatan Allah Ubangiji ya raya shi bisa turbar addinin musulunci.

Na auri matata duk da likita ya sanar dani cewa baza ta taba haihuwa ba, yanzu mun haihu tare – Magidanci

Wani magidanci dan Najeriya mai suna Marvel Iyen ya hau shafinsa na Facebook, ya bayyana yadda ya auri matarsa, duk da likita ya sanar dashi cewa baza ta taba haihuwa ba.

Sai dai wani labari mai dadi shine, ko watanni shida ba ayi da daurin auren ba amaryar ta dauki ciki, inda a yanzu haka suka haifi kyakkyawar yarinya.

Ga dai labarin mutumin a kasa:

Bari na baku labari akan aure na da zai baku mamaki matuka.

Kimanin watanni 6 kafin ni da matata Iyen muyi aure, ta fara yi mini korafin ciwo a cikinta. Da farko mun yi watsi da lamarin, amma sai ciwon ya cigaba da karuwa, sai na ce mata taje ta ga likita domin ayi mata gwaji.

Bayan sun gama gabatar da gwaje-gwajen su, sai likita yake bayyana mana cewa ita juya ce baza ta taba haihuwa. Wannan labari ya tada mata hankali matuka.

Ta kira mahaifiyarta da ‘yar uwarta ta sanar da su wannan labari, suma hankalin su ya tashi. Sai suka ce mata kada ta sanar dani halin da ake ciki, saboda suna tsoron cewa zan jaanye maganar auren.

Na tuna lokacin da ta zo wajena da sakamakon asibitin idonta cike da hawaye, ta rike hannuna ta ce Baby kayi hakuri, likita ya ce ba zan taba haihuwa ba.

A lokacin naga yadda ta cika da tsoro, ita kanta tayi tunanin zan janye maganar auren. Kawai sai na rike hannuntaa, saboda ba zan iya jurewa na ga halin da take ciki ba, na rungumeta, na yi mata rada a kunne, nace mata ba wai ina so na aureki dan na sama ‘ya’ya bane, ina so na aure ki ne saboda ina sonki, kuma ina so na kare rayuwata tare da ke, idan ba za mu iya haifar ‘ya’ya ba sai muje gidan marayu.

Ta cika da mamakin abinda ta ji nace, ta tsaya a gabana kawai ta cigaba da kukan murna.

A zancen gaskiya wannan shine daya daga cikin hukunci dana yanke a rayuwata mai wahalar gaske, kwarai da gaske SO gaskiyane.

A lokacin hatta ‘yan uwana na kasa gaya musu, hatta mahaifiyata na kasa gaya mata, saboda bana so su kashe mini guiwa.

Bayan watanni shida muka yi aure, na riga na gama sawa a zuciyata cewa baza mu taba haihuwa ba, saboda haka ko kadan dama ni ban damu ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Facebook

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe